Murray da Djokovic sun kai wasan Q/Final a gasar Dubai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Andy Murray da Novak Djokovic

Andy Murray ya kai zagayen wasan dab da kusa da na karshe a gasar Tennis ta Dubai, bayan da ya doke Marco Chiudinelli.

Murray wanda shine na uku a duniya, ya doke Marco ne da mai 6-3 6-4 a sa'a daya da minti 23.

A yanzu haka dai Murray zai fafata ne da Tomas Berdych a wasan dab da kusa da na karshe.

Novak Djokovic shima dai ya kai zagayen wasan dab da kusa dana karshe bayan shima ya doke Sergiy Stakhovsky.

Novak Djokovic ne dai na daya a fagen Tennis a duniya.