'Yan wasan Ingila uku sun samu rauni

Hakkin mallakar hoto Reuters

'Yan wasan Ingila, wato Chris Smalling da Daniel Strurridge da kuma Steven Gerrard za su yi jinya na wani dan lokaci saboda raunin da su ka samu a wasan sada zumuncin da Ingila ta buga da Holland a filin Wembley.

Holland dai ta doke Ingila ne da ci uku da biyu a ranar Laraba a wasan na farko da tawagar kasar ta buga tunda Fabio Capello ya ajiye aikinsa.

A yanzu haka dai kocin 'yan wasan 'yan kasa da shekarun 21 ne wato Staurt Pearce ke jagorancin tawagar kasar na wucin gadi, kuma hukumar kula da kwallon kafar kasar ta ce ba za ta yi gaggawan nada wani sabon koci ba.

Wani babban jami'i a hukumar, Sir Trevor Brookings ya ce hukumar za ta yi nazari na kusan watanni biyu domin lallubo kocin da ya kware domin maye gurbin da Fabio Capello ya bari.