Fifa za ta bincike Bharain saboda kwallayen 10 da ta zura

Hakkin mallakar hoto FIFA

Fifa ta fara binciken nasarar da Bharain ta yi a kan Indonesia da kwallaye goma da nema a wasan share fage na taka ledea a gasar cin kofin duniya.

Bahrain dai na bukatar ta zura kwallaye tara ne kafin ta kai zagaye na gaba a wasanni share fagen.

Har wa yau kasar Qatar dai ta kawar da wannan dama saboda ta buga kunen doki da Iran inda su ka tashi 2-2.

"Fifa za ta yi bincike game da wasan da sakamakon da aka samu". Mai magana da yawun Fifa.

"Za'a yi binciken ne saboda wani yanayi na dabam da aka samu, wanda kuma ake shakku akai. Muna son mu karawa mutane kwarin gwiwa ne a wasan kwallon kafa."

Fifa ta ce akwai yiwuwar an yi coge a wasan, wanda kuma ta fara bincike a kai.

Har yanzu dai Hukumar kwallon kafa ta ce tana jiran rahoton alkalin wasa ne kafin ta ci gaba da bincike.