Aiki da Chelsea jidali ne —Scolari

Luiz Felipe Scolari Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Tsohon kocin Chelsea, Luiz Felipe Scolari

Tsohon kocin Chelsea, Luiz Felipe Scolari, ya ce aiki a karkashin Roman Abramovich zai zama jidali ga duk wanda ya zama kocin kungiyar ta Chelsea.

A yanzu haka dai Abramovich na neman koci na takwas ne tun shekara ta 2003 bayan da ya ya sallami Andre Villas-Boas ranar Lahadi.

"Duk wanda ya gaji [Villas-Boas] zai shiga jidali", in ji Scolari, wanda ya yi watanni bakwai yana horar da Chelsea a kakar wasanni ta 2008 zuwa 2009.

Scolari ya kuma kara da cewa, "[Sallamar Villas-Bois] abu ne mai daure kai, ko da yake ni bai daure min kai sosai ba saboda abin da na fuskanta lokacin da nake aiki da kungiyar ta Chelsea".

Scolari, wanda ya yi nasarar cin Kofin Duniya tare da Brazil a shekara ta 2002, ya fara aiki a Stamford Bridge ne a lokacin bazara na shekara ta 2008.

Kafin nan, a watan Satumban shekara ta 2007, Jose Mourinho, wanda ya jagoranci kungiyar ta Chelsea ta yi nasara a gasanni da dama, ya bar Stamford Bridge din aka kuma maye gurbinsa da Avram Grant, wanda aka kora duk da kokarin da ya yi na kai Chelsea wasan karshe na Gasar Zakarun Turai.

An dai tube Scolari ne bayan ya jagoranci kungiyar ta buga wasanni talatin da shida, kuma tana matsayi na hudu a teburin Gasar Premier.

A lokacin sallamar shi dai an yi ta rade-radin cewa wadansu 'yan wasa ne ba su ji dadin yadda yake tafiyar da kungiyar ba—matsalar da aka ce Villas-Boas ma yana fuskanta.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Korarren kocin Chelsea, Andre Villas-Boas

Tsohon kocin na Portugal ya kuma yi amanna cewa yawan korar kwaca-kwacai da Chelsea ke yi a jini ne.

"A Ingila, akwai kulob-kulob irin su Arsenal, inda Aresne Wenger ke horar da 'yan wasa shekara da shekaru; amma kuma gasanni biyu ko uku kacal ya yi nasarar lashewa", in ji Scolari, sannan ya kara da cewa "su Chelsea nasu salon daban ne".

Karin bayani