Formula 1: Red Bull ta karaya da McLaren

Christian Horner Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban kungiyar Red Bull, Christian Horner

Shugaban kungiyar tseren motoci ta Red Bull, Christian Horner, ya bayyana direban kungiyar McLaren Jenson Button da cewa shi ne barazana mafi girma ga kungiyarsa a gasar tseren motoci ta Formula One a bana.

Horner ya kuma ambaci sunayen Lewis Hamilton na McLaren da Fernando Alonso na Ferrari a matsayin wadanda za su taka rawar gani.

"Lewis zai yi kokari matuka bana, saboda shekarar na da muhimmanci a gare shi; Jenson Button kuma ya yi abin a-zo-a-gani bara; Alonso Fernado ma ba za a bar shi a baya ba don kuwa kwararren direba ne", in ji Horner.

Sai dai kuma ya kara da cewa zakaran gasar na bara, Sebastian Vettel, wanda dan kungiyarsa ne, zai bayar da mamaki.

Horner ya kuma yi hasashen cewa ba za a samu tazara mai yawa ba a tsakanin wadanda za su yi nasara a gasar ta bana.

Karin bayani