An damfari hukumar gasar Olympics ta bana

Filin wasa na Olympics a Landan Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Filin wasa na Olympics a Landan

An shaidawa wata kotu a Landan cewa wadansu mutane sun damfari hukumar da ke gina wuraren da za a gudanar da gasar Olympics ta bana fam miliyan biyu da dubu dari uku, ko dalar Amurka miliyan uku da dubu dari shida.

Masu shigar da kara sun shaidawa kotun cewa mutanen su takwas sun yi shigar burtu ne suka ce suna aiki da kamfani gine-gine na Skanska wanda ya gina wuraren wasanni da dama, suka kuma bukaci hukumar ta tura kudaden kamfanin wani sabon asusu, suna masu cewa kamfanin ya sauya bankin da yake ajiya.

Daga bisani ne dai aka gano cewa sabon asusun na wani mutum ne mai suna Ansumana Kamara, wanda ya yi kokarin rufen sawun kudaden ta hanyar rarraba su zuwa asusun abokan damfararsa, kafin ya yi yunkurin aikewa da wani cakin kudi fam miliyan biyu zuwa wani asusu a Najeriya.

An dai zargi mutanen da halalta kudaden na haram.

Karin bayani