Aiki a Chelsea a kai kasuwa —Redknapp

Harry Redknapp Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kocin Tottenham, Harry Redknapp

Kocin Tottenham, Harry Redknapp, ya ce ba ya sha'awar maye gurbin Andre Villas-Bois a Chelsea.

Redknapp, wanda kuma ake zaton yana iya zama kocin Ingila bayan tafiyar Fabio Capello a watan Fabrairu, ya ce samun aikin horar da 'yan wasan Chelsea buri ne na wadansu mutane.

"[Chelsea] kulob ne da mutum zai iya jagoranta su ciwo gasa saboda mai kulob din ba ya shakkar kashe kudi—suna da filin wasa mai kyau da kwararrun 'yan wasa; aiki ne da kowa zai yi sha'awa, sai dai da sharadi: dole ne mutum ya yi nasara, in kuma bai yi ba to ba zai kai labari ba.

"Aiki ne da kowa zai yi sha'awa amma ni dai kam, don ta ni a kai kasuwa", in ji Redknapp.

Karin bayani