UEFA ta tuhumi Wenger da aikata ba-daidai-ba

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto
Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

Hukumar Kwallon Kafa ta Turai, UEFA, ta tuhumi kocin Arsenal, Arsene Wenger, da laifin aikata ba daidai ba.

Wannan mataki na UEFA ya zo ne bayan Wenger ya furta wadansu kalamai dangane da alkalin wasa dan kasar Slovenia, Damir Skomina, bayan fitar da Arsenal daga Gasar cin Kofin Zakarun Turai ranar Talata.

Wenger ya tunkari Skomina ne bayan busa usir a karshen wasan, yana zargin alkalin wasan da baiwa AC Milan bugun falan-daya fiye da kima, duk da cewa kulob din na Italiya sun sha kashi da ci uku ba ko daya.

Bayan wasan, ya bayyana cewa: "Ban yi farin ciki da alkalin wasan nan na yau ba, saboda ina jin ya bayar da bugun falan-daya fiye da kima.

"Da zarar sun fadi sai ya ba su bugu, da suka fahimci haka kuma, sai suka yi ta amfani da damar suna zubewa".

A shekarar da ta gabata dai UEFA ta haramtawa Wenger zama kusa da 'yan wasansa har sau biyu.

Karin bayani