Dan wasan Wolves zai yi hutun mako uku

Terry Connor
Image caption Kocin Wolves, Terry Connor

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Wolves, Karl Henry, ba zai buga wasa ba har tsawon makwanni uku ko hudu sakamakon raunin da ya yi a cinya yayin wasansu da Fulham ranar Lahadi.

Dan wasan Wolves din Dave Edwards ma dai ba ya buga wasa saboda raunin da ya yi, al'amarin da ya sa suka kirawo David Davis, dan wasan da suka baiwa Chesterfield aronsa.

A cewar kocin kungiyar ta Wolves, Terry Connor, "An duba Karl, an kuma tabbatar da cewa ba zai buga wasa ba har tsawon makwanni uku ko hudu".

Kocin ya kuma shaidawa shafin intanet na kungiyar, wadda ta ke cikin kungiyoyin da ke fuskantar yiwuwar sullubowa daga Gasar Premier, cewa, "Muna sa ido sosai a kan David, kuma mun ga yana kokari matuka a kakar wasanni ta bana, saboda haka wannan wani zabi ne da muke da shi".

Karin bayani