Muna sha'awar Van Perise, in ji Roberto Mancini

Roberto Mancini Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kocin Manchester City, Roberto Mancini

Kocin Manchester City, Roberto Mancini, ya jaddada sha'awarsa ta sayen dan wasan Arsenal, Robin van Persie, sai dai ya ce ya yi amanna dan wasan zai fi so ya ci gaba da zama a Emirates.

Kwantiragin dan wasan mai shekaru ashirin da takwas, wanda ya ci kwallaye talatin da biyu a kakar wasa ta bana, zai kare ne a shekarar 2013, don haka ya dakatar da tattaunawa a kan sauya sheka har sai nan gaba.

"Muna sha'awar 'yan wasa masu kwazo", in ji Mancini, "Ina kuma ganin dukkan manyan kungiyoyin kwallon kafa na kwadayin samun van Persie.

"Dan wasan gaba ne mai hazaka, amma ina tunanin zai fi so ya ci gaba da zama a Arsenal".

Mancini ya kuma kara da cewa a ganinsa idan van Persie ya bar Arsenal to za a samu babbar matsala a Emirates.

A bara ma City sun dauke Samir Nasri daga Arsenal, sannan a 'yan shekarun baya sun karbo Gael Clichy, da Kolo Toure, da Emmanuel Adebayor daga Gunners din.

Karin bayani