Lukas Podolski zai koma Arsenal daga Cologne

Arsene Wenger Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kocin Arsenal, Arsene Wenger

BBC ta samu rahotannin da ke nuna cewa Arsenal ta amince ta shiga wata yarjejniya wadda za ta baiwa dan wasan gaba na Jamus Lukas Podolski damar komawa kulob din daga Cologne.

Rahotanni sun nuna cewa Arsenal din za ta biya dan wasan mai shekaru 26 fam miliyan goma da dubu dari tara domin kwantiragin shekaru hudu a kan fam dubu dari duk mako.

Sai an auna lafiyar Podolski sannan kuma ya amince da wadansu ka'idoji kafin a kammala yarjejeniyar.

A watan da ya gabata dai kocin Cologne Stale Solbakken ya bayyana cewa mai yiwuwa Podolski ya bar su, kuma tattaunawa a kan haka ta yi nisa.