Murray ya sha mamaki a hannun Garcia-Lopez

Andy Murray Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Andy Murray

Zakaran wasan tennis na Burtaniya, Andy Murray, ya sha mamaki a hannun dan wasan tennis na casa'in da biyu a duniya, Guilllermo Garcia-Lopez, wanda ya ba shi kashi a wasansa na farko na gasar Indian Wells.

A haduwa biyun da suka yi a baya, Murray bai sha kashi a hannun dan wasan na Spaniya ba; sai dai wannan karon ya sha mamaki, inda aka gama da shi a cikin sa'a guda da minti arba'in.

A wasansa na farko a irin wannan gasa bara ma, Murray ya sha kashi a hannun dan wasan Amurka, Donald Young.

Shan kashin da ya yi watanni goma sha biyun da suka gabata wani bangare ne na koma-bayan da Murray ya samu sakamakon doke shi da Novak Djokovic ya yi a karawar karshe ta gasar Australian Open.

Karin bayani