Kenya ta jarraba sauye-sauyen tseren motoci

Daya daga cikin motocin tsere na Formula One Hakkin mallakar hoto video
Image caption Daya daga cikin motocin tsere na Formula One

An jarraba sauye-sauyen da Hukumar Kula da Tseren Motoci ta Duniya, wato FIA, ke shirin yi ga hanyoyin tseren motoci yayin Gasar Tseren Motoci ta Kenya a karshen makon da ya gabata.

Sauye-sauyen dai sun tanadi maye gurbin gajerun kwanonin da ake amfani da su yanzu da wadanda ake amfani da su da can masu tsawo sosai.

Wakilin BBC a Kenya ya ruwaito cewa bayan da Kenya ta kasa samun damar karbar bakuncin daya daga cikin gasannin tseren duniya ne dai hukumomin tsere na kasar ke ta hankoron gamsar da hukumar ta Duniya ta maido da Tseren Safari cikin gasannin tseren na duniya.

Saboda haka ne ma suka yi caraf suka yi sauyi a yanayin gasar tasu don ta dace da sauye-sauyen hukumar ta FIA.