Shugaban Kwallon Brazil ya yi murabus

Ricardo Teixeira da Ronaldo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ricardo Teixeira da Ronaldo

Dadadden Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Brazil, CBF, kuma mai jagorantar shirye-shiryen karbar bakuncin Gasar cin Kofin Kwallon Kafa na Duniya ta 2014, Ricardo Teixeira, ya yi murabus daga mukaman biyu.

Wata sanarwa daga hukmar ta CBF ta ce jami'in mai shekaru sittin da hudu, wanda ya sha fama da zarge-zargen almundahana, ya sauka daga mukaman nasa ne saboda dalilai na rashin lafiya.

A wata sanarwar ban kwana, Mista Teixeira ya yi korafin cewa ya sadaukar da lafiyarsa don gudanar da aikinsa, amma kuma ya sha suka a lokutan da aka yi rashin nasara an kuma manta da shi a lokutan da abubuwa suka yi dadi.

Ricardo Teixera ne dai ke shugabancin hukumar kwallon kafar ta kasar da ta fi ko wacce shahara a kwallon kafa a duniya a shekaru ashirin da ukun da suka gabata.

Sai dai a 'yan shekarun baya an tilasta masa kare kansa daga zarge-zargen almundahana a matsayinsa na shugaban hukumar ta CBF da kuma mamba a kwamitin zartarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA.