Ina son Tevez ya fara taka leda - Micah Richards

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Carlos Tevez

Ina son Tevez ya fara taka leda - Micah Richards

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Micah Richards, ya ce zai so ya ga Carlos Tevez ya fara taka leda saboda shi kadai zai iya cin wasa.

Kungiyar Kwallon kafa ta Manchester City na bayan Manchester United da maki daya bayan da kungiyar Swansea ta doke ta da ci daya mai ban haushi a karshen makon da ya gabata.

''Akwai wasanni a karkar wasannin bara inda Carlos yasa mu kayi nasara'' a cewar Richard kuma a wasa irin wadda mukayi da kungiyar Swansea zai sa mu iya lashe wasan da ci daya ba ko daya''

'' Sai dai wuka da nama na hannin kocin Manchester City amma ni dai zanso naga ya fara taka leda''

Tevez, wanda ya zura kwallaye 44 a cikin raga a karawa 69 a gasar Premier a lokacin da ya fara taka leda a Manchester City bai sake taka wa kungiyar leda ba tun bayan lokacinda koci Roberto Mancini ya zargeshi da kin motsa jiki a gasar zakarun turai inda suka sha kashi a hannun Bayern Munich a watan Satumban bara.