Ba zan bar Los Blancos ba —Mourinho

Jose Mourinho
Image caption Kocin Real Madrid, Jose Mourinho

Kocin Real Madrid, Jose Mourinho, ya ce zai ci gaba da zama a Los Blancos ko da kungiyar ba ta yi nasarar zuwa wasan daf da na kusa da na karshe a Gasar Zakarun Turai ba.

Kungiyar ta Real Madrid, wadda ke jagorancin Gasar La Liga, za ta kara ne da CSKA Moscow ranar Laraba a zagaye na shida na Gasar Zakarun Turai, tana kuma bukatar kyakkyawan sakamako kafin ta samu damar wucewa, kasancewar an tilasta mata yin kunnen doki daya-da-daya a bugun farko na wasan.

Duk da haka, Mourinho ya jaddada cewa sakamakon bugu na biyu na wasan ba zai yi tasiri a kan makomarsa a Real Madrid ba.

"Makoma ta a Real Madrid ba ta dogara a kan sakamakon wannan wasan na Gasar Zakarun Turai ba; in dai ba kungiyar ba ce ta ce a'a, ko CSKA ta ci mu zan ci gaba da zama na a nan", in ji Mourinho.

Tsohon kocin na Chelsea ya ce ya zaku a buga wasan na ranar Laraba a Santiago Bernabeau, ko da yake ya jaddada cewa CSKA Moscow ba kanwar lasa ba ce.

Karin bayani