Arsene Wenger ya yabawa 'yan wasan Arsenal

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsene Wenger Kocin Aresenal

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya yabawa kwazon da 'yan wasansa suka nuna a lokacin da suka zura kwallo a cikin ragar Newcastle ana gab da kare wasan da bangarorin biyu suka buga.

Kungiyar ta Arsenal wacce ke baya ta farga inda ta samu lashe wasan da ta buga karo na hudu a jere a gasar Premier.

Wenger yace'' Dalilin da yasa mu ka dokesu shi ne mun nuna kwazo sosai wurin ganin mun yi nasara''.

''Ban taba tunanin cewa ba za mu ci wasan ba. Na fadawa mataimakina cewa muna bukatar mu sake kai hari kuma zamu ci''

Kungiyar Arsenal dai na bayan abokiyar hammayarta watau kungiyar Tottenham da maki goma a karawar da suka yi a watan daya gabata, sai dai yanzu Arsenal din na baya ne da maki daya kawai bayan nasarorin da suka samu a wasannin da suka buga.

An fara zirawa 'yan wasan Aresenal kwallo da farko a filin wasa na Emirate a ranar Litinin a karawarsu ta hudu a lokacin da Hatem Ben Arfa ya zura kwallo cikin ragar Arsenal amma bayan minti guda Robin Van Persie ya mayarda martani da kawallo ta 44 da ya zura a wasanni 45 na baya-bayan nan da ya buga a gasar Premier.