Terry ya yi watsi da zargi a kan 'yan Chelsea

John Terry
Image caption John Terry

Kyaftin din Chelsea, John Terry, ya yi watsi da zargin da ake yi cewa ikon da 'yan wasa ke da shi a kan kungiyar ne ya sa aka kori tsohon kocin kungiyar, Andre Villas-Boas.

Mai tsaron gidan Arsenal, Wojciech Szczeny, da tsohon kocin Chelsea, Luiz Felipe Scolari, sun soki 'yan wasan Chelsea da cewa su suke tafiyar da al'amura a kungiyar.

Sai dai Terry ya ce babu gaskiya a kalamansu: "Muna cin wasa kuma muna shan kaye tare, a kan haka dukkanmu muna da alhaki game da sakamakon da muke samu".

Ya kuma kara da cewa: "Game da cewa wuka da nama na hanun manyan 'yan wasan kungiyar kuwa, wannan magana ce da ba ta da tushe kuma wannan ra'ayi ne na mutanen da ke waje saboda Roman Abramovich da sauran shugabannin kungiyar ne ke daukar mataki a kan al'amuranta".

An dai kori Villas-Boas ne bayan ci daya mai ban haushi da West Bromwich Albion ta yiwa Chelsea a watan da muke ciki; sai dai tun bayan wannan lokaci kungiyar ta Chelsea ta doke Birmigham City a gasar cin kofin FA da kuma Stoke a gasar Premier a karkashin jagorancin kocin wucin-gadi Roberto Di Matteo.

Karin bayani