Liverpool ba za ta karaya ba —Gerrad

Image caption Dan wasan klub din Liverpool Steven Gerrard

Dan wasan Liverpool Steven Gerrard ya bukaci sauran 'yan wasan kulob din da kada su yi kasa a gwiwa bayan da suka doke Everton.

Gerrard ya bukaci 'yan wasan na Liverpool su yi amfani da nasarar da suka samu ranar Talata a kan Everton da ci uku ba ko daya, don tabbatar da cewa nasararsu a gasar Premier ta dore da kuma kawo karshen koma-bayan da kungiyar ke fuskanta a 'yan kwanakin nan a gasar ta Premier.

Kwallaye uku da Gerrard ya zira a cikin ragar Everton ne dai suka baiwa kungiyar damar kaucewa shan kaye a karo na hudu a jere.

A cewarsa, ''Abin takaici ne yadda muka kasa taka rawar gani a gasar Premier''.

''Muna bukatar ganin cewa bamu yi kasa a gwiwa ba ta yadda zamu ci gaba da samun nasara''

Kungiyar ta Liverpool dai ta sha kashi a hannun Manchester United, da Arsenal, da kuma Sunderland a wasanni ukun da suka buga na baya-bayan nan.