Kungiyar kwacakwacai ta soki Abramovich

Roman Abramovich Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Roman Abramovich

Kungiyar Kwacakwacan Gasar Premier ta yi kakkausar suka a kan mai kungiyar Chelsea, Roman Abramovich, saboda manufarsa ta yawan korar kwacakwacai.

Shugaban kungiyar Kwacakwacan, Howard Wilkinson ne dai ya soki Abramovich saboda sallamar Andre Villas-Bois da ya yi bayan kocin bai cika wata tara yana horar da 'yan wasan kungiyar ta Chelsea ba.

A cewar Wilkinson, "A bayyane ta ke cewa Roman Abramovich bai san bambancin da ke tsakanin 'yan wasan kwallon kafa masu tagomashi da kuma gina kungiya mai nasara ba.

"Shaida ta nuna cewa kungiyoyi masu nasara su ne wadanda aka gina su bisa cikakkaken tsari da kuma kyakkyawar manufa ta lokaci mai tsawo; su ne kuma suke da hangen nesa a kan inda suke son zuwa da hanyar da za su bi su je can".

Wilkinson ya kuma yi kira ga Abramovich ya dauki darasi daga tsofaffin zuma irinsu Barcelona, da Manchester United, da kuma Arsenal.

Karin bayani