An kwace fasfon kocin 'yan kwallon Ghana

Goran Stevanovic Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Goran Stevanovic

Rahotanni sun nuna cewa Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Serbia ce ta kwace fasfon kocin Ghana, Goran Stevanovic, shi ya sa ma bai samu damar zuwa wata muhimmiyar tattaunawa da Hukumar Kwallon Kafa ta Ghana ba a kan makomarsa.

Wadansu masharhanta dai na ganin kwace fasfon ba zai rasa nasaba da takaddamar diflomasiyyar da ke tsakanin kasashen biyu ba, sakamakon amincewar da Ghana ta yi da kasar Kosovo, al'amarin da bai yiwa Serbia dadi ba.

Rahotanni sun ce kocin ya aikewa wani jami'i a Hukumar Kwallon ta Ghana sakon text yana shaida masa halin da yake ciki.

Ana dai sa ran Stevanovic zai isa kasar ta Ghana ranar Alhamis don halartar tattaunawar wadda aka shirya yanzu za a gudanar ranar Juma'a.