Raunin Tiger Woods ba mai tsanani ba ne

Tiger Woods Hakkin mallakar hoto ALLSPORTGetty Images
Image caption Tiger Woods

Fatan da Tiger Woods ya ke yi na shiga gasar Golf ta Masters a watan Afrilu zai tabbata, bayan da ya samu labarin cewa raunin da ya yi a kafa bai yi munin da aka zata tun farko ba.

Dan wasan mai shekaru talatin da shida ya janye daga Gasar WGC-Cadillac a karshen mako saboda raunin, wanda ya tilasta masa kauracewa wani gangare na gasar a bara.

Sai dai bayan daukar hoton raunin, an gano cewa ba mai tsanani ba ne.

Tun watan Nuwamban shekara ta 2010 dai Woods bai ci wata muhimmiyar gasa ba, amma kuma ya nuna alamun kumarinsa ya fara farfadowa bayan da ya lashe Gasar Kalubale ta Duniya a watan Disamban da ya gabata, sannan kuma ya zo na biyu bayan Rory McIlroy a Gasar Honda Classic.