Roberto Di Matteo ya yabawa 'yan Chelsea

Roberto di Matteo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Roberto di Matteo ne ya maye gurbin Andre Villas Boas

Kocin rikon kwarya na klub din chelsea Roberto di Matteo ya yabawa banjintar da 'yan wasansa suka nuna bayan da suka lallasa Napoli da ci 4-1 domin kasancewa cikin kungiyoyi takwas na karshe a gasar zakarun Turai.

Kwallon da Branislav Ivanovic ya zira a cikin ragar Napoli a karin lokaci ita ce ta baiwa Chelsea damar samun nasara bayan kwallayen da Didier Drogba da John Terry da Frank Lampard suka zira.

''Mun san sai mun dage sosai sannan za mu iya yin nasara amma kowa ya nuna bajinta sosai''.acewarsa

Klub din Chelsea dai yanzu ya bi sahun klub din APOEL, Barcelona da Bayern Munich da Benfica da Marseille da AC Milan da kuma Real Madrid domin kasancewa cikin klub takwas na karshe.

Chelsea dai tana fuskantar kalubale a karkar bana kuma an kori kocin klub din Andre Villas Boas bayan data sha kashi daga hannun klub din West Brom.

Sai dai kawo yanzu da sauran rina a kaba ga kulb din na Chelsea yayin da suke neman kasancewa cikin klub-klub hudu a gasar Premier da kuma zakaraun turai.