Ministan Wasannin Najeriya ya gana da FIFA

Mallam Bolaji Abdullahi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ministan Wasanni na Najeriya, Mallam Bolaji Abdullahi

Ministan Wasanni kuma Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa a Najeriya, Mallam Bolaji Abdullahi, da Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, Alhaji Aminu Maigari, da Sakataren Hukumar, Barrister Musa Amadu, sun gana da shugabannin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, wato FIFA, ranar Alhamis da safe.

Shugabannin na FIFA da suka halarci zaman sun hada da Shugaban Hukumar, Sepp Blatter, da Sakatare Janar Jerome Valcke, da Daraktan Hukumomin Kwallon Kasashe, Thierry Regenaff, da kuma jami'in yada labarai, Oliver Bert.

A lokacin ganawar, wadda aka yi a hedkwatar FIFA da ke Zurich a kasar Switzerland, Ministan ya mikawa Sepp Blatter kudurin da aka cimma a tsakanin bangarorin da ke takaddama a harkar kwallon Najeriya.

Mallam Bolaji ya shaidawa shugabannin na FIFA cewa dukkan bangarorin sun sasanta rikicin da ke tsakaninsu tun ranar Talata, har ma sun amince su janye dukkan korafe-korafe daga gaban kotuna.