Champions League: Chelsea za ta kara da Benfica

Kocin Chelsea da dan wasansa Drogba Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Chelsea da dan wasansa Drogba

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea za ta kara da kulob din Benfica a gasar cin kofin zakaru na nahiyar turai a matki na kwata-final.

Chelsea ce za ta fara kai ziyara gidan Benfica a zagaye na farko.

Idan Chelsea ta yi nasara, za su hadu da wanda ya yi nasara a wasan kwata-final da za a kara tsakanin AC Milan da Barcelona, inda za a yi karawr farko a gidan Chelsea.

A sauran kungiyoyin da suka rage a gasar, Apoel Nicosa za ta kara da Real Madrid, Marseille kuma za ta fafata da Bayern Munich.

Kulob din na Chelsea mai mazauni a London ya kai ga matakin kwata-final ne bayan ta samu nasara a kan kulob din Napoli.

Wasannin da za a kara:

Talata 27 ga Maris

Benfica V Chelsea

Apoel V Real Madrid

Laraba 28 ga Maris

Marseille V Bayern Munich

AC Milan V Barcelona

Karin bayani