Ghana ta kori kocinta, Goran Stevanovic

Goran Stevanovic Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Goran Stevanovic

Bayan an dauki tsawon lokaci ana tadabburi da kai-komo, a karshe Hukumar Kwallon Kafa ta Ghana (GFA) ta kori kocin tawagar 'yan kawallon kasar, Goran Stevanovic.

Hukumar ta yanke shawara ta kori kocin dan kasar Serbia ne duk kuwa da cewa saura watanni goma kwantiraginsa ya kare.

Alkadarin Stevanovic ya karye ne bayan kasar ta Ghana ta sha kashi a hannun Zambia a wasan kusa da na karshe na Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka ta 2012.

Stevanovic ya shaidawa BBC cewa: "Tambaya guda na yi—ko zai yiwu in ci gaba da aiki—sai suka ce a'a.

"Abin ya ba ni mamaki saboda a gani na kaiwa wasan kusa da na karshe ba karamin abu ba ne".

Hukumar ta GFA ta ce ta umurci mataimakin Stevanovic, Kwesi Appiah, ya karbi ragamar tawagar ta wucin-gadi kafin a samu koci na dindindin.

A watan Janairun 2011 ne dai aka danka alhakin horar da tawagar ta Ghana a hannun Goran Stevanovic, wanda ya dauki alkawarin lashe Kofin Kasashen Afirka.

Stevanovic ya ce a lokacin wani zama da hukumar ta GFA ta yi ne ranar Juma'a aka bayyana masa cewa bukatar aikinsa ta zo karshe, sannan aka jaddada masa hakan ranar Litinin lokacin da ya gana da hukumar tare da lauyansa.

Karin bayani