A zakulo dan kallon da ya jefi Samba —Anzhi

Christopher Samba Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Christopher Samba (a gefen hagu)

Kungiyar Anzhi Makhachkala ta Rasha ta bukaci Lokomotiv ta Moscow ta zakulo dan kallon da ya jefi dan kasar Congo, Christopher Samba, da ayaba ranar Lahadi.

Wannan al'amari, wanda Anzhi ta bayyana shi da cewa "wauta ce", ya faru ne lokacin wasan da masu masaukin baki, wato Lokomotiv suka lashe da ci daya mai ban haushi.

A wata sanarwa da ta fitar, Anzhi ta ce "An tabbatar mana cewa wakilan Lokomotiv za su bincika, kuma za a zakulo wanda ya aikata wannan abu a hukunta shi".

Samba ya ce abin da ya bakanta masa rai shi ne al'amarin ya faru ne kusa da kananan yara.

A halin da ake ciki kuma, Lokomotiv ta ce za ta wallafa sakamakon bincikenta a shafinta na intanet.

A karshen watan Fabrairu ne dai Samba ya koma Anzhi daga Balckburn Rovers.

A bara ma, an jefi wani dan wasan na Anzhi, dan Brazil Roberto Carlos, har sau biyu a Saint Petersburg da Samara.