United za ta musanya Berbatov da Modric

Dimitar Berbatov Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dimitar Berbatov

Manchester United za ta tsawaita kwantiragin Dimitar Berbatov a wannan makon, da zimmar musayarsa da dan wasan Tottenham, Luka Modric.

Kwantiragin dan wasan zai kare ne a karshen kakar wasanni ta bana, amma kuma rahotanni sun nuna cewa kungiyar ta United za ta tsawaita kwantiragin da shekara guda da nufin hana shi tafiya wata kungiyar da araha.

Kungiyar dai ta yi amanna za ta iya samun abin da ya kama daga fam miliyan shida zuwa takwas kuma za ta yi kokarin amfani da shi don sayo Modric.

Tottenham dai za ta bukaci akalla fam miliyan arba'in ta sayar da dan wasan nata, kudin da ake ganin United ba ta da halin biya; saboda haka ne za ta hada da Berbatov.

Har yanzu dai babu tabbas a kan ko Tottenham za ta amince ta karbi Berbatov din.

Karin bayani