Owen Coyle ya yi gajeruwar hira da Muamba

Owen Coyle
Image caption Kocin Bolton, Owen Coyle

Kocin Bolton, Owen Coyle, ya ce ya yi 'yar gajeruwar hira da Fabrice Muamba a karo na farko tun bayan da ciwon zuciya ya kama dan wasan.

An garzaya da dan wasan mai shekaru ashirin da uku Asibitin Kirji na Landan ne bayan ya yanke jiki ya fadi yayin wasan Gasar Cin Kofin FA tsakanin Wanderers da Totenham ranar Asabar.

A cewar Coyle, "Har yanzu dai da sauran aiki a gaba, amma kuma wannan alama ce mai kyau.

"Daga abin da na gani ranar Asabar ban yi tsammanin za a samu irin wannan ci gaban ba".

Likitoci dai sun ce suna ci gaba da sa ido a kan dan wasan.

Ranar Litinin aka bayyana cewa ko da yake yana kan siratsi, yanayin Fabrice Muamba ya inganta tun da har ya iya yin numfashi da kansa.

Wacce zai aura, Shauna Magunda, ta aike da sakon twitter tana cewa: "Allah Ya karbi addu'o'inku, jama'a. Mun gode sosai".

Karin bayani