A inganta matakan kula da lafiyar 'yan wasa —Mancini

Roberto Mancini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kocin Manchester City, Roberto Mancini

Kocin Manchester City, Roberto Mancini, ya ce kamata ya yi a rika duba lafiyar 'yan wasan Gasar Premier duk shekara.

Kocin dan Italiya dai na jin cewa tantance lafiyar 'yan wasan na yanzu ba ya bayar da cikakken sakamako.

A cewar Mancini, "Lokacin da na ga matakan kula da lafiyar 'yan wasanmu shekaru biyu da suka wuce, hankali na ya tashi. Akwai bukatar a inganta su".

Mancini ya furta wadannan kalamai ne bayan Shugaban Gasar Premier, Richard Scudamore, ya ce za a yi garambawul ga matakan kula da lafiyar 'yan wasa bayan da ciwon zuciya ya kama Fabrice Muamba.

Ma'aikatan lafiya dai sun kwashe mintuna shida suna kokarin farfado da Muamba bayan ya yanke jiki ya fadi yayin wasan Bolton da Tottenham ranar Asabar.

Dan wasan ya samu irin kulawar da ya samu ne sakamakon sauye-sauyen da Gasar ta Premier ta yi ga al'amuran kiwon lafiya bayan kokon kan mai tsaron gida na Chelsea Petr Cech ya tsage a 2006.

Sai dai duk da haka, kocin na City ya nace cewa matakan kula da lafiyar 'yan wasa a Ingila ba su kai na Italiya inganci ba, yana mai cewa akwai bukatar duba lafiyar 'yan wasa akalla sau biyu duk shekara.

Karin bayani