Vidic ya kusa dawowa wasannin share-fage

Nemanja Vidic Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Nemanja Vidic

Nemanja Vidic ya bayyana cewa nan ba da jimawa zai koma buga wasannin share-fagen kakar wasanni na Manchester United bayan wani dogon hutu sakamakon raunin da ya yi.

Tun watan Disamba ne dai, bayan da ya yi rauni a gwiwa a wasan Gasar Zakarun Turai da United ta sha kashi a hannun Basel, dan wasan mai shekaru talatin ya fara zaman benci.

Tun bayan da aka yi masa tiyata a gwiwar ce kuma Vidic ya takaita ga motsa jiki kawai.

Yayin da yake hutu ne dai kyaftin din na United ya shaida yadda abokan wasansa suka samu nasarar shan gaban Manchester City a saman teburin Gasar Premier.

Vidic ya yi amanna cewa karon battar Manchester (tsakanin United da City) na 30 ga watan Afrilu ne kawai kalubalen da United ke fuskanta daga kungiyoyi bakwai na saman tebur; hakan kuwa a ganinsa na nufin United ta dauki hanyar lashe Gasar ta Premier a karo na ashirin.

Karin bayani