Ba za mu tilastawa 'yan wasa ba —Bolton

Image caption Owen Coyle

Kocin kungiyar kwallon kafa na Bolton, Owen Coyle, ya ce duk dan wasan da ya ce ba shi da nutsuwar buga wasa a karawar da za su yi da Balckburn ranar Asabar ba zai sa shi ya buga wasan ba.

Wasan dai shi ne na farko a Gasar Premier tun bayan da dan wasan tsakiya na Wanderers Fabrice Muamba ya yanke jiki ya fadi, a sanadiyyar ciwon zuciya a lokacin Gasar Cin Kofin FA a wasansu da Tottenham.

"Mun yi matukar mamaki da ya kawo yanzu. Amma kawowarsa yanzu abu ne da ya ba mu kwarin guiwa, kuma muna jaddada cewa har yanzu yana cikin matsanancin hali a asibiti", inji Coyle.

Ya kuma bayyana cewa ya yi magana da iyalin Muamba, kuma sun dage cewa lallai sai Bolton ta buga wasan na ranar Asabar.

"Duk da cewa abu mafi muhimmanci shi ne farfadowar Fabrice", inji kocin, "za mu fita fili kuma za mu yi wasa bakin kokarinmu".