Karon battar United da City: Fatan Ferdinand

Rio Ferdinand Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mai tsaron baya na Manchester United, Rio Ferdinand

Mai tsaron baya na Manchester United, Rio Ferdinand, ya ce zai so kungiyar tasa ta kammala yin nasarar lashe Gasar Premier kafin ta kara da Manchester City a karshen watan Afrilu.

Yanzu haka dai United na gaban City a kan tebur ne da maki daya kawai.

A cewra Ferdinand, "Ko wanne sakamako zai iya sauya yanayin teburin ta ko wacce fuska, ko wanne wasa na da matukar muhimmanci, saboda haka yana da muhimmanci mu yi nasara a sauran wasannin da suka rage mana".

Dan wasan na United ya kuma kara da cewa: "Ina fatan za mu yi nasara a duk wasanninmu kafin mu kara da City".

Karin bayani