Carlos Teves na da muhimmanci —Mancini

Carlos Tevez Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Carlos Tevez

Kocin Manchester City, Roberto Mancini, ya ce Carlos Tevez zai taka wata muhimmiyar rawa wajen samun nasarar kungiyar a Gasar Premier bayan hutun watanni shida.

An mayar da Carlos kusan saniyar ware tun bayan zarginsa da aka yi cewa ya ki motsa jiki domin taka leda a wasan da Man City ta sha kashi a hannun Bayern Munich da ci biyu ba ko daya.

Tevez ne dai ya yi sanadiyyar nasarar da Samir Nasri ya samu ta zura kwallo ta biyu a wasan da Man City ta doke Chelsea, abin da ya rage tazarar da ke tsakanin City da Manchester United a teburin Premier.

"Nan da kwanaki goma ko mako biyu, Carlos zai kara samun karfin jikinsa kuma hakan na da muhimmanci a gare mu", inji Mancini.

"Tara ya ke bai cika goma ba, amma ya san kwallo sosai, kuma abu ne mai muhimmanci da ya taimakawa Samir ya zura kwallo.

"Idan yana wasa ya san lokacin da ya dace ya karbi kwallo. Dan wasa ne mai muhimmancin gaske, amma akwai bukatar ya dan huta na mako biyu zuwa uku", a cewar Mancini.

Mancini ya yi amanna cewa nasarar da Man City ta samu a kan Chelsea ka iya taka muhimmiyar rawa a yunkurin City na lashe Gasar Premier.