Newcastle ta taka rawar gani a wasanta da West Brom

Newcastle ta yi nasara kan West Brom Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Newcastle ta yi nasara kan West Brom

Newcastle ta taka rawar gani inda ta bi West Brom har gida ta doke ta da ci 3 da 1.

Nasarar na ta ya daga makin ta ya zo daidai da na klub din Chelsea in banda banbancin kwallaye a raga.

Hatem Ben Arfa ya yi Krossing ga Papiss Cisse, shi kuma bai yi wata wata ba ya zura kwallo ta ukku a ragar West Brom cikin sauki.

To saidai wata tangarda da aka samu a bayan Newcastle ya baiwa Shane Long damar zura kwallo guda.

An tashi ne dai Newcastle na da ci 3 yayinda West Brom ke da ci daya.