Yan wasa shida ne ake fargabar sun rasu a Afirka ta Kudu

wasan rugby Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption wasan rugby

A kasar Afirka ta Kudu, akwai fargabar cewa mutane shidda ne a cikin yan wasan kulob din Rugby na kasar suka rasu, bayanda ruwa ya tafi da su a lokacinda suke linkaya.

An samu gawar mutum guda, akwai kuma mutane biyar da suka bace.

Alamarin ya auku ne sa'ilin da yan wasan ke linkaya a teku, bayan sun gudanar da atisaye a kusa da gabar tekun dake Port Elizabeth.

Yan wasa da dama ne aka samu damar kubutar da su.

Mutanen dai yan wasan Rugby ne a kulob din Motherwell na Afirka ta Kudu.