Ahly za ta kauracewa wasannin cikin gida a Masar

yan wasan al-ahly Hakkin mallakar hoto AP
Image caption yan wasan al-ahly

Babbar kulob din birnin Alqahira na kasar Masar, ta ce za ta kauracewa duk wani wasan kwallon kafa na cikin gida.

Ta ce ta yanke wannan shawarar ce saboda matakin da hukumar kwallon kafar kasar ta dauka na dakatar da al-Masry na tsawon shekaru biyu.

Al-Ahly ta yi imanin cewa sassaucin yayi yawa ga kulob din da ta dauki nauyin wasan league din aka halaka masoya kwallon kafa kimanin 70 a watan jiya.

Ahly ta ce ba za ta sake buga wasan cikin gida ba har sai an musaya mahukunta na wucin gadi a hukumar kwallon kasar EFA.

Haka kuma al-Ahly na shirin karar al-Masry a gaban kuliya, game da gazawar ta na samar da tsaro a wasan.