Kalaman batanci ya jefa wani dalibi gidan kaso

Fabrice Muamba Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Fabrice Muamba

Wata kotu a Birtaniya ta yankewa wani dalibi zaman gidan kaso, a sabili da kalaman batanci da ya sa a shafin internet kan Fabrice Muamba, dan wasan kwallon kafar da ya samu bugun zuciya a lokacin da suke wasa a watan jiya.

Liam Stacey ya amsa laifin sa na wallafa kalaman batanci na banbancin launin fata, kuma zai shafe kwanaki 56 a kurkuku.

Tuni dai Muamba ya farfado daga bugun zuciyar, to amma har yanzu ya na sashen kula da marasa lafiya na gaggawa.

Wasan tsakanin Bolton da Tottenham wanda aka dakatar saboda bugun zuciyar na Muamba, za a sake bugawa a daren yau.