An yanke wa dan wasan rugby makonni 8 saboda cizo

wasan rugby
Image caption wasan rugby

Kotu a Birtaniya ta yankewa Dylan Hartley dan wasan Rugby na kasar Engila haramcin yin wasa na tsawon makonni takwas saboda cizon Stephen Ferris da yayi a dan yatsa.

Kyaptin din na kulob din Northampton, ba zai samu damar buga wasan da za su yi a ranar 14 ga watan Mayu ba, manufa zai iya buga wasan da Engila za ta buga a Afirka ta Kudu idan ya na daya daga cikin yan wasan da aka zaba.

Ferris dai wanda aka ciza, ya jawo hankalin alkalin wasa ne Nigel Owens bayan da alamarin ya auku a bayan idonsa.

A na sa bangare Hartley ya bayyana rashin gamsuwar sa da hukuncin, kuma ya na da damar daukaka kara.