Kasadar Chelsea a wasanta da Benfica ta biya

Roberto di Matteo Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roberto di Matteo

Mai horar da yan wasan kulob din Chelsea na wucin gadi Roberto di Matteo, ya ce matakin da ya dauka na zaban yan wasa, wadanda suka taka leda a gasar zakarun turai na kusa da na karshe, ya nuna cewa ya san abin da yake yi.

Mai horar da yan wasan na Blues ya yi gaban kan sa, ya bar manyan yan wasa kamar Didier Drogba, da Frank Lampard da Michael Essien a benci, amma duk da haka, Chelsea ta yi nasara kan Benfica da ci daya da nema.

Salomon Kalou ya tabbatar da kwarewar sa, bayan da zabin sa ya bada mamaki, inda ya zura kwallo guda daya tilo da ta baiwa Chelsea nasara.

Di Matteo ya ce, "ba na ganin cewa kasada na dauka, to amma a rayuka wani lokacin dole ka dau aradu da ka".