Man U na samun fifikon alkalan wasa, inji Vieira

Patrick Vieira Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Patrick Vieira

Daya daga cikin jamian kulob din Manchester City wato Patrick Vieira ya ce abokan hamayyar su wato Manchester United na samun fifiko daga wurin alkalan wasa.

Kalaman na sa na zuwa ne kwanaki biyu bayan da aka hana kulob din Fulham bugun daga kai sai gola mai cike da takaddama a wasan da Manchekter United ta yi nasara da ci daya da nema.

Sakamakon wasan ya baiwa United maki 3 kan Manshester City wadda a baya ita ce ke saman tebur.

"idan United ta buga wasa a gida, ta na samun fifiko wanda sauran kulob-kulob ba sa samu," inji Vieira a hirar su da BBC.

Ana saura wasanni 8 a kawo karshen kakar wasan Premier na bana, a halin yanzu City na bayan United da maki ukku, saidai Vieira yayi imanin cewa za su yi nasara.