Shirin gasar cin kofin Afirka na gab da haduwa a Afirka ta Kudu

Afirka ta Kudu
Image caption Afirka ta Kudu

Biranen Afirka ta Kudu dake fatan karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka a badi, za su san matsayin su a ranar 4 ga watan Afrilu.

Garuruwa shidda ne suka bayyana sha'awar su ga kwamitin dake shirya gasar.

A baya dai an shirya cewa za su gabatar da bayanin yadda za su karbi bakuncin a ranar Jumua, to amma suka nemi a ba su karin lokaci.

Afirka ta Kudu dai ta samu damar karbar bakuncin wasan na cin kofin Afirka ne, bayan da aka bayyana Libya wadda ita ce a baya ya kamata ta karbi bakuncin gasar na shekarar 2013, da cewa ba ta da cikakken tsaro.

Biranen Johannesburg, da Cape Town, da Polokwane, da Rustenburg da kuma Nelspruit suka bi sahun biranen da aka buga wasan cin kofin duniya, wato Bloemfontein, da Port Elizabeth da Durban, wurin neman karbar bakuncin gasar.