BBC navigation

Djokovic ya doke Murray a wasan karshe na zakarun Tennis a Miami

An sabunta: 1 ga Aprilu, 2012 - An wallafa a 20:08 GMT
novak djokovic

novak djokovic

Na daya a duniya a fagen wasan Tennis wato Novak Djokovic ya doke Andy Murray inda ya daga kofin zakarun Tennis na Miami Masters.

A shekarar 2009 a irin wannan wasa, Murry ya doke Djokovic a wasan karshe, to amma a wannan karo, labarin ya sha banban.

Djokovic bai yi kasa a gwiwa ba ko kuma nuna wata alamar tausayi a karon farko na wasan da ci 6 da daya.

Murray ya yunkuro a turmi na biyu a wasan, to amma dan kasar ta Serbian bai fito yin wasa ba, inda ya doke dan Birtaniya a fagen karshe na wasan.

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.