Mancini yayi hasashen Man U za ta ci kasa

Roberto Mancini Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Roberto Mancini

Mai horar da yan wasan kulob din Mancheter City Roberto Mancini yayi amannar cewa abokan hamayyar su Manchester United za su rikito da maki, wanda zai baiwa City damar hayewa saman tebur.

Bayan da City ta tashi ukku da ukku da Sunderland, United za ta iya sake hawa da maki biyar kan City, idan ta yi nasara kan Blackburn a ranar Litinin.

"ina gani United za ta yi canjaras a ranar Litinin," inji Mancini.

A halin yanzu dai City ta na da maki 71, yayinda United ta ke da maki 73, ana saura wasanni 8 a kammala kakar bana.