Tottenham ta lallasa Swansea da ci 3 da daya

tottenham Hakkin mallakar hoto huw evans agency
Image caption tottenham

Kwallayen Emmanuel Adebayor guda biyu sun taimakawa Tottenham ta samu nasarar da take matukar bukata kan Swansea City a wasan Premier League.

Rafael van der Vaart ne ya fara fasa ragar Swansea daga yadi 20.

To saidai ba da dadewa ba Gylfi Sigurdsson ya farke wa Swansea, suka dawo kunnen doki, kafin Adebayo ya yunkuro kenan, inda ya zura kwallaye guda biyu a ragar Swansea.

Kwallayen na Adebayo, sun taiamakawa Tottenham ta farfado, bayan wasanni biyar a jere ba tare da ta cin wasa ba.

A yanzu dai Tottenham ce ta hudu a kan tebur din wasan Premier na Ingila.