Isreala ta kama dan wasan Olympic na Palasdinawa

Israela
Image caption Israela

Rundunar sojin Israela ta ce ta kama wani mai tsaron gida na tawagar Palasdinawa yan wasan Olympic na kwallon kafa bisa zargin sa da harbin sojojinta.

Israela ta ce ta kama Omar Abu Rois ne tare da wasu mutane 13 bisa zarginsu da hannu wurin harbi kan dakarun Israela.

To saidai babu wani dan Israela da ya samu ko da kwarzane sakamakon harbin da Isrealar ta ce an kai kan dakarun na ta a sansanin yan gudun hijira dake Amari a gabar yammacin kogin Jordan.

Darektan kulob din Amari, wato Jihad Tomalah ya tabbatar da kama Omar Abu Rois.