"Dalglish ba zai bar Liverpool ba", inji Mark Lawrenson

kenny dalglish Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption kenny dalglish

Kenny Dalglish ba zai daina horar da yan wasan Liverpool ba, inji tsohon dan wasan kulob din Mark Lawrenson.

Liverpool dai ta ci kofin Carling, kuma a yanzu su na matakin wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin FA, to amma ta sha kashi da ci biyu da nema a wurin Newcastle, wanda shi ne wasa na shidda a cikin wasannin Premier na Ingila bakwai da take gaza samun nasara.

Lawrenson, wanda a baya yayi wasa da Dalglish a shekarun 1980, ya shaidawa BBC cewa, ba ya tunanin cewa Dalglish zai tafi, kuma ba ya tunanin za a kore shi.

Liverpool dai wadda ta koma ta takwas a tebur din wasan Pemier, za ta hadu da Everton a wasan kusa da na karshe na gasar FA a Wenbley a ranar 14 ga watan Afrilu.