Halin Man U ne cin wasa a karshe, inji Alex Ferguson

Sir Alex Ferguson Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sir Alex Ferguson

Mai horar da yan wasan Manchester United Sir Alex Ferguson, ya ce nasarar da yan wasan sa suka samu a karshen wasan su da Balckburn, abu ne da United dama ta saba yi.

Da farko dai alamu na nuna cewa United za ta yi canjaras ne a Ewood Park, kafin Antonio Valencia da Ashley Young suka yunkuro ana saura minituna goma a hura usur din karshe na wasan.

Nasarar dai ta baiwa Manchester United damar sake tserewa Manchester City da maki biyar a wasan Premier na Ingila.

Ferguson ya ce "dare ne mai tsawo da muka jajirce, kuma daga bisani, mun samu ladan kokarin da muka yi".