An halaka wasu jami'an gwamnati a harin kunar bakin wake a Somalia

Bam ya tashi a Somalia Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Bam ya tashi a Somalia

Wata fashewar da aka samu a sabon gidan wasan kwaikwayo a Mogadishu, babban birnin Somalia, ta hallaka mutane bakwai tare da raunata wasu da dama.

Daga cikin wadanda suka rasu har da shugaban hukumar kwallon kasar da kuma shugaban Kwamitin Wasannin Olympics na Somaliar.

Abdul Rahman Osman, kakakin gwamnatin Somaliar, ya soki wadanda suka kai harin.

Ya ce, “Haka tsarinsu yake, abin da suke son gani ke nan - Al ka'ida a Somalia.

“Gurinsu shi ne su hana mutane samun walwala a rayuwarsu, su hana abubuwan shakatawa.

Kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Al Shabaab, wadda ta dauki alhakin kai harin, ta soma amfani da hare-haren kunar bakin wake ne tun lokacin da aka fatattake ta daga birnin Mogadishu a watan Agustan 2011.

Karin bayani