Za mu iya doke Barcelona, inji di Matteo

Kulob din Chelsea Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kulob din Chelsea

Kocin kulob din Chelsea na riko Roberto di Matteo ya hakikance cewa, za su kirkiro da wani shirin yadda za su yi galaba kan kulob din Barcelona a wasan kusa da na karshe na zakarun turai.

Idan Chelsea na son zuwa wasan karshe, to dole ne sai ta doke Barcelona a wasan kusa da na karshe.

Di Matteo ya jaddada cewa Chelsea ba ta tsoron haduwa da Barcelona, wadda ita ce mai rike da kofin zakarun turai, kuma ita ce aka fi tsammanin cewa za ta sake daga kofin.

To saidai wani koma baya ga Chelsea shine raunin da kyaptin din kulob wato John Terry ya yi a wasansu da Benfica wanda har ya kai ga musaya shi da Gary Cahill.

A na sa bangare, John Terry ya ce ya na haki idan ya na wasa saboda raunin da ya yi a hakarkarin sa, to amma zai ci gaba da yi wa Chelsea wasa.